Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kungiyoyin Kare Hakkin Dan Adam Sun Bukaci Sudan ta Hukumta Masu Hannu A Yakin Darfur


Gamayyar kuniyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa FIDH ta yi kira ga gwamnatin hadakar kasar sudan da ta yi amfani da wanna damar wajen hukumta wadanda ke da hannun wajen kisan kare dangi da aka yi wa jama’a a yankin Darfur na kasar, kusan shekaru 17 kenan, bayan kazamin yaki da aka yi da ya ci rayukan mutane da dama.

Sabuwar gwamnatin hadakar ta kasar Sudan ta sha alwashin kawo karshen rikicin yankin da ya hada da yankin Darfu inda rikici tsakanin ‘yan tawaye da masu goyon bayan gammati wanda ya haddasa mutuwar mutane 300,000 yayin da dama da miliyan 2.5 kuma suka tsere daga gidanjensu tun a shekarta ta 2003 kamar yadda rahoton majalisar dinkin duniya ya tababtar.

Yanzu haka dai an daure tsohon shugaban kasar Umaru Albashir a gidan yari na tsawon shekaru 2 saboda zargin cin hanci da rashawa baya ga sammacin kama shi da kutun duniya mai hukumata manyan lefuka da ke birnin Hugue ta bayar kan zargin yin kisan kare dangi, laifukan yaki, da kuma cin zarafin dan adam.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu