Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Kwamitin Tsaro Na MDD Zai Yi Zama Kan Gwajin Makami Mai Linzami Na Korea Ta Arewa


A wannan Laraba ce ake sa ran kwamitin tsaro na MDD zai gudanar da wani zama bisa bukatar Amurka, kan gwajin makami mai linzami da kasar Korriya ta arewa ta yi .
Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa zaman kwamitin tsaro zai gudana ne a wannan Laraba a yayin da aka kasa samun fahimtar juna tsakanin hukumomin Washington da Pyongyang kan raba tsibirin koriya da makaman nukiliya.

A ranar Lahadin da ta gabata ce kamfanin dillancin labaren kasar Koriya ta arewa ya sanar da cewa kasar ta yi gwajin wani makami mai linzami cikin nasara a tsibirin Suha.

A makon da ya gabata ma kasar ta harba wani makami mai linzami a lardin Hamgyong.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu