Pastor yohana buru ya bayyana haka ne a yau 25/12/2019 a wajen bikin kirismeti a cocin sa da ke gwagi villa da ke nan cikin garin kaduna, a yayin ziyarar da wakilan kaduna Press suka kai mai tare da yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky da ga janibobi da ban da ban, a fadin kasar nan.

Pastor ya kara da cewa: yana da kyau al'umma kirista suyi anfani da wannan lokaci na bikin kirismeti dan taimakon al'umma, ta hanyar bayar da tufafi da ciyar da miskinai da ziyara wadanda da suke Kurkuku da sauran mabukata, da yin addu'a ga marasa lafiya.

Sannan ya kara da cewa: lokacin Kirsimeti lokacin Salama ne, lokaci ne na sa sanci da juna, da zaman lafiya, a fahimci juna, sannan a ingata mu'amala da zaman take wa, lokaci ne da zamu dauki darasi, da yiwa juna a dalci.

Ya cigaba da cewa: a cikin wadannan abubuwa da ya kawo bawai ga kirista kawai ba, abubuwa ne mai muhimmanci da mai imani zai yi anfani da shi, wasu na Kurkuku ba dan sunyi laifi ba, zalunci ne yasa a ka rufe su. Sannan wasu na kurkukun sunyi laifin amma sunyi nadama a tina da su.

A karshe pastor ya yi kira ga Malam addini da su ji tsoron Allah da su dai na raba kan al'umma, sannan ya yi addu'a da Allah ya kawo mana shugaban ni, na garin masu kunar al'ummar su ba masu wawaso dukiyoyin talakawa ba.