Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

M D D Ta yi Kira Da A Gudanar Da Taro Na Farko Kan Wadanda Suka Rasa Muhallinsu

Hukumar kula da yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta buka ci a gudanar da taro na farko a irinsa da zai kunshi gwamnatocin kasahen duniya da kungiyoyin faraaren hula da manyan Attajirai domin bullo da hnayoyin da za’a bi wajen taimakawa sama da mutane miliyan 10 da suka rasa gidajensu sakamakon barkewar yaki, tarzoma da talauci da dai sauran matsaloli na daban.

Shugabar hukumar ta yan gudun hijra Gillian Trigggs ta bayyana cewa ana sa ran gudanar da taron kasa da kasa kan yan gudun hijirar ne daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Decembar nan da muke ciki a birnin Janeva , babban manufar shirya taron shi ne samar da hanyoyin da za’a tallafawa miliyoyin mutane da suka rasa mahallansu saboda da dalilai daban – daban.

Kuma ana sa ran sama
da mutane 3000 da suka hada da ministocin gwamnatocin kasahen100 ne za su
halarci wanann taron musaman wadanda suka fi fama da matsalar, kamar kasashen
Mayanmar , Afghanistan, Sumaliya, Sudan ta kudu, Siriya, da Venuzuela

Post a Comment

0 Comments

Close Menu