Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Tir Da Dokar Zama Dan Kasa Ga Wanda Ba Musulmi Ba A Indiya


Offishin kare hakkin dan Adama na Majalisar dinkin duniya ya nuna damuwarsa matuka game da sabuwar dukar zama dan kasa a Indiya da a fili karara tana nuna ban-banci da wariya ne, inda aka cire musulmi daga cikin wadanda dokar za ta shafa, An yi taho mu gama tsakanin Yan sanda da daliban jamio’I da suka fito zanga zangar nuna amincewa da wannan sabuwar doka da majalsiar dokokin kasa ta amince da ita.

Har ila yau dubun dubatan Alummar musulmi a fadin kasar ta Indiya ne suka fito kan tituna bayan kammalar sallar juma’a domin nuna adawa da wannan sabuwar doka da za ta share hanyar zama dan kasar Indiya ga wasun kungiyoyin Addinai guda 6 da ke makwabtaka da kasahen Bnagaladash Pakistan da Afganisatan da kuma mayar da dubban baki da suke zaune a kasar ba bisa ka’aida ba, su zama yan kasa.

Sai dai Fira ministan kasar Narendra Modi dan Addinin Hindu ya bayyana cewa dokar wadda ta samu amincewar majalisar dokokin kasar za ta kare yan tziraru ne dake wadannan kasashen, sai dai kakakin hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD Jeremy Laurence ya bayyana sabuwar dokar amatsayin ta wariya da nuna bangarenci, domin bata yi la’akari da irin wannan kariyar ga musulmi da sauran kanan addinai ba akasar.

Tuni pira ministan kasar Japan Shinzo Abey ya suke ziyarar day a shirya kaiwa Indiya saboda tarzomar da ta barke a yankunan dake Arewa masu gabashin kasar wanda anan ne aka shirya gudanar da taro tsakaninsa da Fira minister Modi.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu