Rahotanni da ke fitowa daga Nigeria sun bayyana cewa Majalisar Wakilai ta kasa ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gudanar da sabon kidayar jama’ar kasar kafin karshen shekara ta 2020, saboda wanda aka gudanar tun a shekara ta 2006 ya tsufa kuma ba shi da wani tasiri game da tsara manufofin siyasa.

Ademorin Kuye dan majalisa wakilai da ya fito daga Jihar Legas karkashin inuwar Jam’iyar APC shi ne ya jagoranci gabatar da daftarin kudurin, ya bayana cewa lamarin abin takaici ne, ya kara da cewa madama ba’a bullo da wani tsarin na yin kidayar jama’a lokaci bayan lokaci kamar yadda ake yin zabe a kasar ba, to fa yan Nigeria za su ci gaba da fuskantar matsalar jinkiri wajen gudanar da kidaya.

Har Ila yau ya ce gwamnati na bukatar bayanai don sanin adadin yaran da aka haifa, da kuma adadin makarantu da Asibitoci da za’a bukata, da kuma ma’aikata nawa ne a kowanne gari da kuma adadin yan kasashen wajen da ke zaune a kasar, domin samar da ingantattun ababen more rayuwa.

Daga karshe ya ce kamata ya yi a rika gudanar da Kidaya sau daya a duk bayan shekaru 10.