Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Majalisar Dokoki A Nigeria Ta yi watsi Da Bukatar Kara Wa’adin Mulki Na shekaru 6 Ga Shugaban Kasa.


Majalisar wakilai ta kasa a Nigeria ta yi watsi da bukatar da aka gabatar na neman a kara wa’adin mulki na tsawon shekaru 6 sau daya, ga shugaban kasa da gwamnaoni da sauran masu rike da mukaman siyasa maimakon shekaru 4 da shuwagabannin da aka zaba suke yi, har sai in an sake lashe zabe kafin su koma a wani waadi na biyu.

Kudurin da dan majalisa John Dyegh na jam’iyar APC da ya fito daga jihar Benue ya gabatar ta shiga karatu na biyu, inda aksarin yan majalisar suka nuna rashin amincewarsu da wannan kuduri.A nashi bangaren dan majalisa Haruna Bello na jam’iyar PAC da ya fito daga jihar Kano ya bayyana cewa kudurin zai iya jawo zargi na wani yunkurin kara wa’adin mulkin shugaban Nigeria Mohammadu Buhari.

Ya ci gaba da cewa da amincewa da shekaru 6 kawai sau daya, zai rufe kofa ga sauran shuwagabannin da suka yi wa’adi daya wajen sake dawowa a wani waa’adi na shekaru 4, don haka kamata ya yi a bar tsarin yadda ya ke na wa’adin shekaru 4 sau biyu.

A nashi bangaren shi ma wani dan majalisar ya bayyana cewa babbar mastalar mu ita ce rashin mutunta dokokinmu, amma Demukuradiyarmu ba ta bukatar waa’adin shekaru 6 ka dai ga masu rike da madafun iko.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu