A wani zama da majalisar wakilan Amurka ta gudanar a jiya laraba ta kada kuri’a mai cike da tarihi inda aka amince da tsige shugaban kasar Donald Trumph saboda da zargin yin amfani da mukaminsa ba yadda ya dace ba, don cimma manufofinsa.

Mafi akasarin majalisar wakilan sun goyon bayan kudurin tsige shugaban kasar , kuma Trumph shi ne shugaban kasar Amurka na Uku da za’a tsige a cikin tarihin kasar sai dai ana ganin akwai yiyuwar tsigewar ya hadu da cikas inda aka kai batun gaban majalisar dattawa inda yan jami’iyar Rebulican da ya fito daga cikinta suka fi rinjaye.

Batun tsige shugaban na Amurka ya kawo tarnaki sosai a fadin kasar inda ya kawo rarrabuwar kai tsakanin alummar kasar tsakanin masu goyon bayan tsige shi da kuma masu adawa da shi,yanzu haka dai shuwagabannin GOP sun sanar da cewa ba za su taba goyon bayan tsige shugaban kasar da suka zaba ba a zaben da aka gudanar a shekara ta 2016 ba.

Shi dai Trumph ana zarginsa ne da yin amfani da mukaminsa ta hanyar matsin lamaba kan shugaban kasar Ukraini wajen bata sunan babban abokin hammayarsa Joe Biden da ake ganin shi ne zai kalubalnceshi a zaben shugaban kasa da za’a gudanar a shekara ta 2020 mai zuwa.