Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Malawi Ta Kori Jakadiyar Tarayyar Turai Daga KasarGwamnatin Malawin ta bai wa jakadiyar tarayyar turai Sandra Paesen lokaci da ta fice daga cikin kasar, saboda tana tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.
Jaridar Nyasa Times ta bayyana cewa; An bai wa jakadiyar tarayyar turai din wa’adin mako guda ne da ta tattara yanata-yanata ta fice daga kasar kasar.

Tun da fari gwamnatin kasar ta Malawi ta aike wa da tarayyar turai wasika da a ciki take zargin jakadiya Paesen da shiga cikin harkokin kasar, inda a watan da ya gabata ma ta shiga wata Zanga-zanga da aka yi a kasar da fada da yi wa mata fyade.
An yi Zanga-zangar ne dai bayan da aka zargi ‘yan sandan kasar da cin zarafin wasu mata a kusa da babban birnin kasar, Lilongwe.

Jakadar ta turai ta kuma yi kira ga gwamnatin Malawin da ta yi Karin bayani akan hakikanin abin da ya faru.

A makon da ya gabata ma dai kasar Benin ta kori jakadan tarayyar turai bisa irin wannan zargi na tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar.

Ba da jimawa ba, kasar Zambia mai makwabtaka da Malawi ta ja kunnen jakadan tarayyar turai saboda shiga cikin harkokin shari’ar kasar, bayan hukuncin daure masu auren jinsi da aka yi, inda jakadan turai din ya ce hukuncin ya yi tsauri.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu