Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Martanin Iran Akan ‘Yan Sahayoniya Zai Zama Mai Karfin Gaske


Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Sayyid Abbas Musawi, ya ce; barazanar da HKI ta ke yi wa Iran tana nuni ne da raunin da take da shi, kuma tabbas martanin da Iran za ta mayar zai zama mai karfin gaske.

Kamfanin dillancin labarun “Irna” ya ambato mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Abbas Musawi yana ci gaba da cewa; Haramtacciyar kasar Isra’ila ta ginu ne akan kwace da mamaya da wuce gona da iri.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya kara da cewa; Bisa dogaro da al’adar gwgawarmaya da tsayin daka da jajurcewa, Iran ba za ta taba yin kasa a gwiwa ba wajen kare kanta da tsaronta, kuma mayar da martaninta zai zama mai karfin gaske ta yadda makiya za su yi nadama.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu