Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Masu Zanga-Zanga A Faransa Sun Ce Babu Batun Sasantawa

kungiyoyin kwadagon kasar Faransa sun tabbatar da ci gaba da zanga-zanga har zuwa lokacin da gwamnati za dawo daga yunkurin da take yi na gyara dokar fansho, kuma babu wata matsaya da aka cimma sanadiyar bukukuwan sabuwar shekara.
Tashar talabijin din France 24 ta nakalto gamayar kungiyoyin kwadago na kasar Faransa na cewa za su ci gaba da zanga-zanga gami da yajin aikin gama gari har zuwa lokacin da gwamnati za ta janye kudirinta na kawo sauyi a sabuwar dokar fansho.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar cikin gidan kasar Faransa a ranar Talata da ya gabata, ta ce daga farka zanga-zangar nuna adawa na gyaran da gwamnati ke son yi a dokar fanshon, kimanin mutane 615 suka fito yayin da kungiyoyin kwadago ke cewa adadin mutanen ya hauwa zuwa miliyan daya da dubu 800.

A zanga-zangar da aka gudanar ta ranar Talata dubban mutane ne suka fito a kan titunan birnin Faransa don ci gaba da yajin aiki da kuma zanga-zangar adawa da sabuwar dokar fansho, lamarin da ya yi matukar gurgunta al’amuran yau da kullum a sassan kasar.

Duk da cewa lamurra na neman rincabewa a kasar, gwamnatin ta bayyana cewar tana nan kan bakanta na yin watsi da bukatar kungiyoyin kwadago, dangane da soke sabuwar dokar sauya tsarin biyan kudaden fansho.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu