MATASAN HARKA ISLAMIYYA SUNKAI ZIYARAR KIRSIMETI A KADUNA...
-KADUNA PRESS

A jiya Laraba 25/12/2019 dan dalin Matasan harkar musulumci karkashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky na yankin kaduna, sun kai ziyarar taya al'ummar kirista murnar zagayowar ranar da aka haifi Annabin Allah Almasihu Isa (a.s) a wata choci mai suna Ife-Oluwa Baptist Church Mando, dake da mazauni a garin Mando, jihar Kadunan Nigeria.

Sidi Ahmad sani kwantagora ne ya jagoranci ziyarar,
A yayin ziyarar sidi yayi bayani gamsasshe ga mahalartan, inda ya bayyana dalilan zuwan nasu, sannan ya bayyanawa al'ummar gurin takaitaccen tarihin ire-iren kamun da mahukumtan kasar Nigeria sukayiwa Sheikh Zakzakiy,
Wannan shine kamu na goma cif-da-cif da aka yiwa Malamin mu, inji shi.
Malam Ahmad ya bayyana cewa munzo ne domin kara kyautata alaka tsakanin mu da ku, koba komi Alqur'ani bai koyar damu daukar makami ba, zaman lafiya ya koya mana, haka zalika Bible bai koyar da kirista daukar makami ba, zaman lafiya ya koya mishi.
Idan kaga musulmi ya dauki makami yana kashe mutane to bayabi koyarwar muslumcin bane, haka zalika kirista shima idan kaga yana kisa to baibi koyarwar addinin shi ba. Inji shi.
Bayan jawabin da Sidi Ahmad ya gabatar cikin harshen turanci, sai aka mikawa Reverend Aderibigbe Edward Oluwafemi shugaban chocin kyautar da aka zo mai dashi, ya karba hannu bibbiyu yaji dadi sosai yayi murna ta gaske.
A ta nashi janibin Mr. Oluwafemi ya nuna jin dadin shi a fili, kun gani ko daman jiya lahadi sanda muna service na fada muku duk inda kaji ance maka Salaam ana nufin aminci ne, amman seka ga wasu idan ance musu salaam kamar basa son amsawa, kuma duk inda kaga musulmi mai son zaman lafiya ne.
Yanzu idan da babu zaman lafiya wadannan musulmin zasu zo nan taya mu murna? Inji shi.
Idan akwai zaman lafiya sai soyayyar juna tazo, soyayya ta aiki a aikace ba wacce kawai za'a fadi a baki ba, da babu soyayya kuna tunanin zamu ga sunzo mana nan ziyara? Inji shi.
Ba zai yiwu kuma mu barku ku tafi haka nan hannu rabbana ba sai mun hadaku da wani dan abin tabawa.
A karshe aka kawowa masu ziyarar drinks da biskits domin su taba.
Akayi Addu'o'i ta bangaren musulmi da kuma su kirista din aka dauki hotuna aka sallami al'umma.
-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-KNPRSCD 06.
-26122019.