Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

MDD Ta Bayyana Hukuncin Da Saudiyya Ta Yanke Kan ‘Makasan’ Khashoggi A Matsayin Izgili


Babbar mai bincike na Majalisar Dinkin Duniya kan kisan gillan Agnes Callamard ta bayyana hukuncin kisa da mahukutan Saudiyya suka ce sun yanke kan wasu mutane da ake zargi da kashe sanannen dan jaridar kasar Jamal Khashoggi a matsayin wani izgili da kuma wasa da hankali na shari’a.

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniyan ta bayyana hakan ne cikin wani sako da ta buga a shafinta na Twitter inda ta ce: An samu maharan da laifi, an yanke musu hukuncin kisa. Amma wadanda suka shirya lamarin suna nan a sake suna wayo inda suke so.

A jiya ne dai wata kotu a Saudiyyan ta ce ta yanke wa wasu mutane biyar hukuncin kisa sakamakon samun su da laifin kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi da aka yi a ofishin jakadancin Saudiyyan a kasar Turkiyya.

Tun dai bayan sanar da wannan hukuncin kwararru da wasu jami’ai na kasashe da cibiyoyi daban-daban na duniya suke sa shakku cikin wannan hukuncin sakamakon yadda kotun ta wanke wasu manyan jami’an tsaron Saudiyyan kuma na kurkusa da Yarima mai jiran gado na kasar Muhammad Bn Salman wadanda ake zargi kai tsaye da aikata kisan musamman Ahmad al-Asiri tsohon mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar da kuma Saud al-Qahtani wani na kurkusa da Yarima mai jiran gadon wadanda ake ganin suna da hannu dumu dumu cikin kisan gillan.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu