Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

MDD Ta Soki Yadda Ake Kara Tura Makamai Zuwa Libiya


Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Kakkausar Suka kan yadda wasu kasashe ke ci gaba da aikewa da makaman yaki zuwa ga bangarorin dake fada da juna a kasar Libiya.

Tashar Talabijin Rusiya Al-Yaum ta ruwaito MDD cikin wani rahoto da ta fitar na cewa tun bayan da dakarun tsaron Libiya masu biyayya da janar Khalifa Haftar suka fara kai hare-hare birnin Tripoli a watan Avrilun da ya gabata zuwa yanzu wasu kasashe da kamfanoni kera makamai ke aikewa da makamai zuwa kasar ta Libiya wanda hakan kuma karya doka ce na wanzuwar makamai a Duniya.

Majalisar ta tabbatar da cewa ita shaida kan yadda ake aikewa da makamai zuwa kasar ta Libiya.

Rahoton ya ce kasashen Jodan da hadadiyar daular larabawa gami da kasar Turkiya na ci gaba da karya dokokin kasa da kasa na hana wanzuwar makamai a Duniya.


Tun a ranar 4 ga watan Avrilun da ya gabata ce dakarun khalifa haftar dake samun goyon bayan kudi da makamai daga kasashen Saudiya da hadadiyar daular larabawa suka fara kai farmaki birnin Tripoli na nufin kwace shi daga gwamnatin hadin kan kasar dake samun goyon bayan kasar Turkiya da kuma kungiyoyin kasa da kasa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu