Ministan na Najeriya, Niyi Adebayo ya jinjinawa yadda aka sami zuba hannun jari a fagen samar da sukari a cikin kasar.

Adebayo wanda ya yi rangadi a cikin harabar kamfanin sarrafa raken, ya ce; hannun jarin da kamfanin Sunti Golden Sugar Estate ya zuba domin samar da sikari a Nigeria, shi ne mafi girma.

Ana sa ran cewa a karshen wannan shekara ta 2019 da ake ciki za a girbe Karen raken da zai kai ton 1,500, tare da samar da aikin yi ga mutane 10,000.