TAKARDAR SANARWAR MANEMA LABARAIIN JI HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA

Harkar Musulunci a Nijeriya ta yi Allah-wadai da mayar da shaikh Zakzaky da mai dakin sa, Malama Zeenah daga wurin da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ke tsare da su zuwa babban gidan-kaso da ke cikin garin na Kaduna a sakamakon umurnin da babbar Kotun ta Jihar Kaduna ta bayar a jiya a yayin da aka hallara a gaban Kotun domin ci gaba da sauraron Shari’ar.

Wannan bayani yana kunshe ne a cikin Takarda Sanarwar Manema Labarai, wadda Shugaban Dandalin Yada Labarai na Harkar Musulunci a Nijeriya, Malam Ibrahim Musa ya sanya wa hannu, kuma ya fitar da ita a jiya ga Manema Labarai.

“Muna kallon duk wani yunkuri na kai Shaikh Zakzaky da mai dakinsa ko’ina ne, matukar ba Asibiti ce ba, wadda ta ke da isassun kayan aiki da kuma kwararrun Likitoci, wadanda za su iya kula da lafiyarsu a matsayin ci gaba da azabtar da su,” in ji Sanarwar Manema Labaran.

Harkar Musulunci a Nijeriya ta nuna rashin gamsuwarta dangane da lamarin gidan yari na Jihar ta Kaduna inda aka mayar da Shaikh Zakzaky da mai dakin sa a jiya, a inda ta bayyana cewa: “Gidan Kurkuku da ke Kaduna ya lalace, kuma ba shi da wurin kula da marasa lafiya. A cikin wannan gidan yari ne wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu a yayin kisan kiyashin Zariya da aka kaddamar a cikin watan Disambar 2015 suka rasa ransu a sakamakon rashin samun cikakkiyar kulawa ta Likitoci. Don haka wannan gidan Yari sam ba shi da Likitoci da kuma Kayan aiki wadanda za a iya yin amfani da su wajen kula da lafiyar Shaikh Zakzaky da mai dakin sa kamar yadda halin lafiyar tasu take cikin tsananin bukata ta gaggawa.”
        Ga dai cikakken bayanin da Takardar Sanarwar Manema Labaran take dauke da shi kamar haka:

*Muna tir da ci gaba da duk wani yunkuri na kara jefa rayuwar Shaikh Zakzaky cikin mawuyacin hali ta kowane irin salo*

Harkar Musulunci a Nijeriya ta yi tir da Allah-wadai dangane da sabon salo na makirci wanda gwamnatin Jihar Kaduna ta yi amfani da shi jiya a Kotu ta hanyar yin amfani da Lauyoyin su domin ci gaba da cutar da Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, da kuma kara sanya shi cikin kangi na azabtarwa da wahalarwa. Wadannan take-take na gwamnatin Jihar Kaduna ba komai ba ne illa mataki na wahalar da Tawagar Lauyoyin da ke tsaya wa Shaikh Zakzaky, wadanda a kowane lokaci suke samun nasara a kan Lauyoyinsu a kan kowane nau’i na Shari’a da suka gudana, ciki kuwa har da babbar nasarar samun hukunci, wanda ya bayar da umarnin a
gaggauta sakin Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah Ibrahim, wadanda dukkanin su har yanzu ake ci gaba tsare su, lamarin da ya saba wa umarnin da wannan babbar Kotu da ke Abuja ta bayar.

Idan za a iya tuna wa gwamnatin Jihar Kaduna ta kwashi kashinta a hannu a yayin Shari’ar da ta gudana tsakanin ta da daruruwan ‘yan’uwa Musulmi almajiran Shaikh Zakzaky a wannan Kotu, don haka ne ta zabi jan-kafa da kuma yin amfani da salo na borin-kunya saboda rashin hujjojin da za ta iya gabatar wa a gaban wannan kotu dangane da kagaggun laifuka na shirme da rashin kan-gado da take tuhumar Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, da aikatawa. Sun ki yarda a ci gaba da gudanar da shari’ar, ta hanyar yin amfani da gabatar da korafi marar dalili da kuma salo na jan-kafa domin kawo cikas ga ci gaban aiwatar da shari’ar sakamakon tabbacin da suke da shi a kan kayin da za su sha saboda rashin hujjojin aikata laifi da za su iya gabatarwa a kan Shaikh Zakzaky da mai dakinsa.

A lokacin da kotu ta ba Shaikh Zakzaky da mai dakin sa damar zuwa Kasar Indiya domin samun cikakkiyar kulawa ta lafiya kamar yadda yanayin halin lafiyar su ke tsananin bukata, gwamnati ta kawo cikas ta hanyar yin kafar-ungulu a kan lamarin. A yayin da suka yi yunkurin kashe Shaikh Zakzaky, ta hanyar yin amfani da jami’an leken asiri na Nijeriya, a cikin Kasar ta Indiya. Lamarin da ya tilasta Shaikh Zakzaky zabar a dawo da shi Nijeriya. Kuma tun lokacin da aka dawo da Shaikh Zakzaky da mai dakinsa daga Kasar ta Indiya ana ci gaba da tsare su ne a
boye. An hana su damar ganawa da Lauyoyinsu, an kuma hana su ganawa da Likitoci, in ban da kawai lokacin da jikin mai dakin Shaikh Zakzaky ya yi tsanani a wurin da ake tsare da su.

Don haka mun yi matukar mamaki dangane da bayani na karya wanda aka gabatarwa da kotu shi a jiya cewa wai ana ba su damar ganawa da Lauyoyin su. Domin kara zalunci a kan zalunci, Lauyoyin gwamnati sun bukaci Kotu ta bayar da umarnin mayar da Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, wadanda suke fama da matsananciyar rashin lafiya zuwa mummunan gidan-kaso da ke cikin garin Kaduna, maimakon kai su wurin da ke da cikakken kayayyakin kula da mara lafiya domin samun damar kula da matsanancin halin rashin lafiya da suke fama da ita.

Gidan Kurkukun da ke Kaduna ya lalace, kuma ba shi da wurin kula da marasa lafiya. A cikin wannan gidan yari ne wasu daga cikin wadanda suka tsira da ransu a yayin kisan kiyashin Zariya da aka kaddamar a cikin watan Disambar 2015 suka rasa ransu a sakamakon rashin samun
cikakkiyar kulawa ta Likitoci. Don haka wannan gidan Yari sam ba shi da Likitoci da kuma Kayan aiki wadanda za a iya yin amfani da su wajen kula da lafiyar Shaikh Zakzaky da mai dakin sa kamar yadda halin lafiyar tasu take cikin tsananin bukata ta gaggawa.

Muna kallon duk wani yunkuri na kai Shaikh Zakzaky da mai dakin sa ko’ina ne matukar ba Asibiti ce ba wadda take da isassun kayan aiki da kuma kwararrun Likitoci wadanda za su iya kula da lafiyarsu a matsayin ci gaba da azabtar da su.

Rashin gurfanar da su jiya a gaban kotu shi ma abin damuwa ne, dalili kuwa a zama na karshe ma da ya gudana ba a kawo su kotun ba saboda tsananin tabarbarewar da halin lafiyar su ke ciki, kamar yadda jagoran Lauyoyin da ke tsaya wa Shaikh Zakzaky, Femi Falana SAN ya bayyana a wancan lokacin.

Don haka muna shelanta Tir da Allah-wadan mu da babbar murya a kan duk wani yunkuri na kara jefa Shaikh Zakzaky da mai dakinsa, cikin mawuyacin hali na kangin wahala da kuma azabtarwa. Muna kara jaddada kiran mu da kuma bukatar mu ta a gaggauta Sakin Shaikh Zakzaky da mai dakinsa ba tare da gindaya masu wani sharadi ba. Ba za mu taba mika wuya ko rusanawa ba, haka nan ba za mu taba gajiyawa ko yin kasa a guiwa ba a kan fafutukarmu ba ta tabbatar da ‘yancin Jagoran mu.

SA HANNU:
IBRAHIM MUSA
SHUGABAN DANDALIN YADA LABARAI NA HARKAR MUSULUNCI A NIJERIYA
SKYPE: Ibrahim.musa42
05/12/2019
Fassarar Zaharaddeen Sani Malumfashi.