Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Muna sheda wa Israila cewar zamu iya kai mata hari har Tel-Aviv.


--- Inji Ministan tsaron Yamen Janar Muhammad Al-Atefi.
-
Tun ranar farko da makiya suka fara kawo mana hari to da Israila aka fara,kuma har yanzu da ita din ake cigaba da kawo mana hari inji Janar Al-Atefi.

Janar din ya sheda wa jaridar "Al-Maseera" cewar "duk harin da makiya suke kawo mana da hannun Israila a ciki,amma har yau basu iya cimma koda muradi daya ba. Don haka muna aheda wa Tel-Aviv cewar muna kallonta,kuma zata iya ganin sakonmu a Tel -Aviv a kowanne lokaci inji Janar Atefi.
-
Muna son Tel-Aviv su sani sarai cewar " Yemen din yanzu ba wacce suka sani bane a baya. Ta yanzu tana da karfin sojan ruwa,na sama da kuma na kasa,kuma muna da mizayil din da zai iya isa har birnin Tel-Aviv inji Janar Atefi. Haka muka rika jan kunnen abokiyar Tel-Aviv din wato Riyadh,amma sai suka dauka barazana ce,amma da suka ga hanmunmu a Riyadh sai suka yarda da gaske muke.

Haka zalika wannan gargadin ma da gaske muke yin shi,kuma muna yi ne daga birnin San'a zuwa kunnen Tel-Aviv inji Janar Muhammad Al-Atefi.

Daga Nasir Isa Ali

Post a Comment

0 Comments

Close Menu