Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Muna tare da Shaikh Mukhtar Sahabi a Zariya - Sulaiman Jibril Richifa.


Sulaiman Jibril Richifa (Allah Ba Mu Sabati) yana daya daga cikin ’yan uwan da suka kubuta daga harin ta’addanci da Sojoji suka kaddamar a Zariya ranar 12 ga watan 12, 2015.

 Wakilinmu Abdullahi Yusuf
Sambo Richifa ya samu zantawa da shi, kuma ya yi masa tilawar yadda waki’ar ta auku, da kuma yadda ya kubuta daga harin, da kuma yadda suka kasance saura su biyu shi da Shaikh Mukhtar Sahabi, Wakilin ’yan uwa na Kaduna a wani waje.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance kamar yadda take.

ALMIZAN: Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?

SULAIMAN JIBRIL RICHIFA: Ni dai sunana Sulaiman Jibril Richifa, wanda aka fi sani da Allah Ba Mu Sabati.

ALMIZAN: Kana daya daga cikin ’yan uwan da aka
yi waki’ar nan a kan idonsu, to za mu so mu ji waki’ar ta same ka a can Zariya ne, ko daga baya ka shiga Zariyar?

SULAIMAN JIBRIL RICHIFA: Lallai waki’ar ba a Zariya ta same ni ba, ranar Asabar ina gida a shagon da nake kasuwanci, sai nake samun labarin cewa an yi waki’a a Gabari, har an samu Shahidai
mutum uku. Can zuwa anjima kuma sai na kara jin waya cewa Zariya babu lafiya, sojoji sun harbi ’yan uwa, kuma har sun tafi da wasu ’yan uwan, kuma yanzu haka ma sun zagaye Husainiyya. To, ina
zaune ina jimamin abin, sai ga wani dan uwa Dahiru ya ce min ka ji abin da ke faruwa a Zariya? Na ce eh, a nan dai muka taru muna jimamin abin,
sai ga Shahid Abdullahi Musa, sai na ba shi labarin halin da ake ciki, ya ce to yanzu ya za a yi to? Muna cikin haka sai ga Ibrahim Dauda, Nura, Abubakar, da kuma Ahmad Muhammad, su ma suna cikin Shahidai, nan dai muka yi ittifaki tunda Zariya babu lafiya, to ba amfanin zamanmu a nan,
shi ne kowa ya je ya shiryo. Muka je muka sami Abdullahi Musa muka kama hanya. Sai duk masu motar da muka ce su kai mu Zariya sai su ce ba
za su ba, wai ana can ana kashe mutane a Zariya.
Don haka sai muka samu masu mashina suka kai mu Wanka, daga nan kuma muka samu mota ta dauke mu ta aje mu a farin masallaci. Daga nan
sai muka dan yi tafiya dai haka, sai muka samu mai Keken Napap ya shiga da mu  Gyallesu. Da muka zo muka ga ’yan uwa dai ana ta tattauna
abin da ke faruwa a Husainiyya. Daga nan dai sai
muka wuce gidan Malam Maina muka yi Sallar Magari ba da Isha, aka ci gaba da addu’o’i. Bayan mun gama sai wani dan uwa yaron Malam
Abdullahi Abbas ya ba mu labarin abin da ya faru a Husainiyya, har ya nuna mana harbin da aka yi masa a kafa. Shi ma daga baya ya yi shahada.  Haka dai ’yan uwa ake ta hira cewa yanzu fa ba
mamaki wata kila a cikin mu din nan akwai Shahidai. Ana cikin haka ne kawai sai muka ji
barikokin Sojoji suna ta buga ganguna alamar za su fita yaki, ba jimawa kuwa sai ga Awwal Mabo ya zo ya yi sallama yana cewa an ce kowa ya shirya ga su nan sun zo Gyallesu, suna shigowa kuwa suka fara ruwan wuta ba kakkautawa.

Daga nan kawai sai muka taso muka tunkare su, to kafin mu je ma wajen tiransifoman gaban gidan Malam Maina an fara dauko Shahidai, haka dai
muka tunkare su ana ta kabbara, wasu kuma suna
“ya Mahdi!” Sun harbo wani gurnat a kan wani shago ya yi wata kara dam! Shi ne sai suka yi amfani da wannan hasken suna ta harbin ’yan uwa. Gaskiya ’yan uwa an sami sabati sosai. Allah ya saka da alheri. Dan uwan da muka zo tare, Abdullahi Musa ya ce mun sun wurgo wani gas mai guba wanda yake dauke numfashi, kuma a wurin da nake akwai ’yan uwan da na iya ganewa
kamar su Awwal K/Mashi, Malam Salisu Soba, Wakilin ’yan uwa na Soba, Malam Sulaiman NEPA, Wakilin ’yan uwa na Richifa, Nura Richifa, Ahmad Muhammad Richifa, wanda a lokacin ma sun harbe
shi a hannu.

Haka dai suka ci gaba da ruwan wuta, abu kama-
kama har wayewar gari, suna harbin ’yan uwa ana dauko su, ga shi ’yan uwan da ke Gyallesu ba wani yawa ne da su sosai ba, domin duk sun
toshe hanyoyin shigowa, kuma ga su su sai kara yawan su ake yi, kuma ana karo masu kayan aiki, kuma sun datse ko’ina ba damar shiga Gyallesu.
Can ma kuma a Husainiyya mana jin karar gurnetin
da suke ta harbawa. Nan suka raba hankalin ’yan uwa, ga nan Gyallesu, ga kuma Husainiyya. A lokaci guda kuma ga kiran wayan da ake ta yi wa ’yan uwa, kai ni sai da na zo ma na daina daukar waya, na ce kawai idan mutum ba zai zo ba, kawai ya daina kiran waya. Don ni a tunani na ya kamata
a ce mutum duk inda yake a kasar nan, to ya ci a ce ya iso Zariya don ba Malam kariya, tunda abin ya dauki lokaci yana faruwa.

Haka dai aka ci gaba, wuraren karfe ukun dare sai labari ya zo cewa sun karo mota 20 na Sojoji, a nan ne ’yan uwa suka yi iya abin da za su iya yi,
kuma lallai ’yan uwa an sami sabati. Don ba su iya shigowa ba sai da Asuba, sai suka yi amfani da fitillun motocinsu gaba daya suka kashe wa ’yan
uwa ido, nan suka yi amfani da dukkanin karfinsua kan ’yan uwa, har dai suka iso jikin gidan Malam. Daga nan kawai ’yan uwa duk sai suka kewaye gidan Malam a tsaye, kowa ya san kawai lokacin shahada ya yi, don ni ma ban taba tunanin
zan wuce wannan lokacin ba, don kusan da fuskata kawai na ga wasu korayen bulat sun wuce ni. A nan jikin gidan Malam an sami Shahidai bila
adadin.

Da gari ya waye Lahadi, da yake an harbi ’yan uwa da yawa, kuma sun ci karfinmu, sai kawai ’yan uwa suka taru a wuri, to shi ne su kuma suke ta
dannowa. A nan suka kusa karar da ’yan uwa. A nan ne ma suka harbi Kanina Abubakar da muke Mama daya da shi, da kuma Usman Aliyu Richifa,
wanda suka harbe shi wajen sau bakwai, da ma sauran ’yan uwa da daman gaske da aka harba.

A lokacin da suka zo jikin gidan Malam a inda nake, ’yan uwa da muka rage ba mu kai mu 20 ba. Wadanda na iya ganewa a wurin sune; Malam Salisu, Wakilin ’yan uwa na Soba, da Shaikh Mukhtar Sahabi, Wakilin ’yan uwa na Kaduna, Abdullahi Jibrin kafin ya yi shahada, da wani Yahya Marabar Jos. To, a nan jikin gidan Malam ma sun
yi barin wuta na fitar hankali. A lokacin akwai wani dan uwa Malam Salisu daga Kaduna, wanda ake ce masa Wakilin Tsoho, ya leko daga gidan Malam ya ce to wanda ya zo ba Malam kariya to ya shigo
cikin gidan Malam don ga su nan za su shigo gidan. To, a lokacin ne na ga Malam Mukhtar Sahabi yana cewa a ba shi mukullin mota ko na
waye ya tunkare su da ita, amma dai ba a samu ba, to kafin ma wani lokaci sun riga sun zagaye mu ta ko’ina, don gidan Malam ma ta baya har sun riga sun fasa katangar suna kokarin shiga.

Ana cikin haka ne kawai sai ’yan uwa suka ji wasu na cewa ai Malam ma ba ya gidan. To da ’yan uwa suka ji haka kawai sai kowa jikinsa ya yi sanyi
saboda Malam aka zo ba kariya, kuma an ce ba ya nan. To, a wannan yanayin ne sai na ji Malam Mukhtar Sahabi ya kira ni, sai muka shiga wani
gidan dalibai a nan kusa da gidan Malam wajen mu 10, amma ina ganin duk sauran da muka shiga da su gidan sun yi shahada sai ni da Malam
Mukhtar kawai muka rage a cikin gidan.

Sojojin suka ce duk wanda ya san ya boye ya fito za mu yi masa sassauci. To shi ne wasu ’yan uwa suka fito, kuma suna fitowa suka harbe su. Mu dai
muna cikin dakin mun yi banza da su. To, daga nan sai Malam Mukhtar ya ba ni wasu addu’o’i ina ta karantawa, shi ma yana karanta wasu. Mun karanta Yasin sau uku. Ya ce kuma mu maimaita wata Aya a cikin Yasin din sau 111. Haka dai muka yi ta addu’o’i. Sai ga Sojojin sun shigo dakin da
muke, amma ba su gan mu ba. Har sau uku suna shigowa ba su gan mu ba, kuma ba wai boyewa muka yi ba.

Muna cikin haka kuma sai aka yi ta kiran Malam Mukhtar din a waya, mai dakinsa ta kira shi, dansa Ukasha ya kira shi, wata ’yarsa ma da ke zaune a
Iran ta kira shi, Malam Kasim Umar Sakkwato shi ma ya kira shi, Malam Abdulhamid Bello da Malam Adamu Tsoho da dai sauran ’yan uwa da daman
gaske sun kira shi. Saboda duk wadanda suka kira shi sai ya gaya min da kuma maganar da suka yi.

Haka dai muka zauna har duhu ya fara yi, sai unguwar ta yi shiru. Sai Malam Mukhtar ya ce bari ya leka ya gani. Da ya leka ya dawo, sai ya ce min dan uwa ba mu da wata mafita fa don ko’ina Sojoji ne. Har ya ce yanzu ga lokacin Salloli ya yi, ya za a yi mu yi Sallah? Ya ce kodayake na san kana
fama da yunwa ko? Na ce masa tun jiya ban karya
ba, amma kuma ba na jin yunwa. Shi ma ya ce min ni ma ban samu na karya ba yau. To, daga nan ya ce min Buraza dole ne fa mu fita daga wurin nan, don zamanmu a nan ba shi da wani amfani, tunda an kona gidan Malam, kuma kowa
ya yi shahada. Wani abu da na lura da shi ga Malam Mukhtar shi ne hankalinsa ko tashi bai yi ba, to ni ma kasancewa ta tare da shi kawai sai na ji na samu natsuwa.

Daga nan dai har kiran wayan da ake mai ya yi yawa sai wayarsa ta dauke, shi ne sai na ba shi waya ta ya sa SIM dinsa. Daga nan ya ce mun Buraza muna tare ban san sunanka ba, sai na gaya masa sunana. Ya ce min daga ina, na gaya masa.
Sai ya ce za mu yi addu’ar fita. Sai ya dinga karanto wasu addu’o’i. Bayan ya gama sai ya ce, to yanzu za mu fita mu biyu ne. Muna fita sai kai ka yi Gabas, ni kuma na yi Yamma. Sai kuma ya ce ka bar ni na fara fita. Sai kuma ya ce kai ka fara fita. Sai ya ce min in cire duk wani alami da za su
gane cewa ni dan uwa ne, duk na cire, ya dauko kum din shi ya ce na tace kaina. Daga nan ya ba ni wata Ayar Alkur’ani ya ce na yi ta karantawa, ya ce; “Insha Allahu ba abin da za su iya yi maka”.

Ya ce; “Ko sun kama ka kar ka ji tsoro, in kuma ka ga wani abu ya faru da kai, to lokacin shahadarka ne ya yi. Kuma ko da ba ka zo nan ba za ka yi”.
To a nan dai muka rabu da Malam Mukhtar. Sai na ga ya dauko wani karamin littafi ya ce min ni ma zan karanta wata addu’a ce yanzu zan fito. Har na fita, sai na dawo na ce masa ta wace hanya zan bi Malam? Sai ya ce min ai ko ta ina Sojoji ne, muna tsakiyarsu ne nan. Sai ya ce min kawai ka fita a
matsayin kai dan makaranta ne. Sai kuma ya ce min ko da yake duk ’yan makaranta sun gama fita, kuma ba ka da wata sheda da ke nuna kai dan
makaranta ne. Ya ce kawai Buraza ka fita, an san ko kai waye kawai, abin da Allah ya yi shi ke nan, in ma shahada ce kawai insha Allah.

To, daga nan ina fitowa kawai sai na gan ni a tsakiyarsu, ko ta ina sune kawai. Ta hanyar da zan wuce a nan suka fi yawa. Kawai sai na nufi wurin.

To, kafin ma na karasa can wajen masu yawan, wasu daga bayana har sun taso sun fara dukana ko ta ina da bakin bindiga har sai da suka kai ni kasa. Kuma suka cire mun riga da wando suka bar ni daga ni sai gajeren wando.

Sai suka ce daga ina nake? Na ce daga can gidan nake. Suka ce kai da waye? Na ce masu ni kadai ne. Suka ce mu je wurin da ka fito mu gani. Muka je, sai ban nuna masu inda Malam Mukhtar yake ba. Da muka dawo sai suka ci gaba da duka na. Sai ga wani Soja ya zo da adda, kawai sai na ji ya dake ni da ita a bayana har sau biyu, har sai da na furta ya Ali! Ana cikin haka sai na ga wani mutum wanda da shi ake komai a cikin ’yan uwa yana cewa ku harbe shi wannan ‘member’ ne a Shi’a.

Da na waigo muka hada ido da shi, kawai sai na ga ya bar wurin.

Haka dai suka ci gaba da duka na, wai sai na nuna masu Oganmu. Wai ana rudar ku ana cewa kun yi mutuwar shahada ko? To, ga shi nan ka ga ’yan uwanka mun kashe su, kuma za mu je mu ci namansu. To, ana cikin haka sai Ogansu ya taso ya ce Wallahi in ba ku daina Shi’ar nan ba duk sai mun kashe ku. Ka ji ko? Ya ce, kai yanzu ba za mu kashe ka ba saboda ka je ka ba da labari. Ni dai kawai abin da nake ta yi a wurin kawai Azkar din da Malam Mukhtar ya ba ni. Can sai Ogan nasu ya ce wa wani Soja dauko min pure water can, sai aka dauko masa, sai ya ce ga shi nan ka wanke kafarka. Na karba na wanke. Sai ya ce sa kayanka ka tafi. Na sa na kama hanya. Ni na dauka ma isgili suke min da na fara tafiya su harbe ni. Kawai sai na ji ba su harbe ni ba, har na shiga wani layi. Da yake duhu ya yi, lokacin mutanen gari ba su gane ni ba, amma duk inda na bi za ka ji wasu daga cikin mutanen gari suna murna da faruwar abin.

Haka dai har na fito Tudun Wada gari ba kowa, kamar an yi shara. Da kyar dai na samu wani mai mashin ya kawo ni Kofar Doka. Daga nan kuma na kira wani abokina ya zo ya kai ni gida. To, ka ji yadda aka yi na fito daga Gyallesu.

ALMIZAN: Muna iya cewa kai ne mutum na karshe da kuka rabu da Malam Mukhtar Sahabi?

SULAIMAN JIBRIN: Lallai kam, kuma sad da muka rabu da shi ko kwarzane babu a jikinsa.

ALMIZAN: A karshe wane sako kake da shi?

SULAIMAN JIBRIN: Sakona shi ne lallai ’yan uwa su sani kowane irin bude wuta aka yi, to ba shi zai sa mutum ya yi shahada ba. Gaskiya a waki’ar nan na kara gaskatawa cewa shahada ta mai rabo ce.

ALMIZAN: Mun gode.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu