Rahotanni daga Burkina Faso na cewa, fararen hula 35 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a lardin Arbinda dake yankin Soum a arewacin kasar.

Bayanai daga kasar sun ce ko baya ga fararen hulan da akwai sojoji bakwai da suka rasa rayukansu a lamarin.

Tun da farko dai maharan sun kai harin kunar bakin wake da mota ne kan sansanin sojin yankin, kafin daga bisani su kai hari kai mai uwa dawabi, a daidai lokacin da kuma wani gungun maharan ke kai wa fararen hula hari.

Mafi yawan fararen hulan da aka kashe wadanda suka kauracewa yankunan su ne sakamakon matsalar tsaro.
Mafi yawan mamatan mata ne a cewar rahotannin.

Rundinar sojojin kasar ta ce an kashe ‘yan ta’adda 80, a fadan da aka kwashe sa’o’I masu yawa ana gwabzawa.Sojojin
sun kuma yi nasara cafke Babura masu yawa da kuma makamman yaki a cewar sanarwar rundinar sojin kasar ta Burkina faso.

Burkina faso kamar sauren makobtanta Nijar Da Mali, sun jima suna fuskantar hare hare na mayakan dake ikirari da sunan jihadi, ciki har da kungiyar dake kiran kanta reshen kungiyar (IS) a yankin.