MUZAHARAR NEMAN A SAKI SHEIKH ZAKZAKIY A DA'IRAR KADUNA...
-KADUNA PRESS.

A yau talata 31/12/2019 ma 'yan uwa musulmi sun sake fitowa domin kara jaddada kiransu ga hukumomin Nigeria akan su gaggauta sakin Jagora Sheikh Zakzakiy da mai dakinsa Malama Zeenat, daga tsarewar haramcin da hukumomin ke yi musu tun a karshen shekara ta 2015.

Tsarewar tasu dai ta biyo bayan farmakin da jami'an tsaron Nigeria suka kai masa a muhallinsa dake cikin unguwar gyallesu a cikin garin Zarian jihar kadunan Nigeria, bayan da suka kashe mabiyansa fiye da dubu 1000+, suka jikkata da dama daga cikinsu kana suka kame daruruwa daga ciki.
Bisa dogaro da kir-kirarren laifi na kage, wai cewa almajiransa sun tsarewa hafsan hafsoshin sojin Nigeria hanya a unguwar G.R.A kofar Hussainiyya a cikin garin Zaria.

Muzaharar wadda 'yan uwan suka gudanar sun farata ne daga Danmani junction da misalin karfe 06:00pm  kuma suka rufe ta a kaura motors duk a kan titin express way na kaduna to Abuja.

Andai fara kuma ankammala lami-lafiya saboda jami'an tsaron nigeria basu halarci gurin ba.
-J.S.A
-KNPRSCD 06
-31122019.