Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Najeriya Ta Yi Watsi Da Rahoton Amurka Kan Tauye 'Yancin Addini


Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wani rahoton Amurka da ke zarfin gwamnatin kasar da tauye 'yancin jama'a na yin addinin da suka ga dama, wanda a karon farko aka Ambato gwamnatin kasar da take hakkin yin addini.

Wata sanarwar da aka fitar a madadin ministan yada labaran Najeriya Lai Mohammed ta ce rahoton ba shi da tushe balla makama.

Sanarwar ta mutanen Najeriya na da cikakken 'yancin yin addininsu a kasar, wanda ya ce kokari ne kawai na neman shafawa kasar kashin kaji.

Gwamnatin ta Najeriya ta ce kungiyar Boko Haram ce kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ce ta saba wa sauran addinai, duk da ikiriarinta na bin addinin Islama.

Game da tsare Sheikh Ibrahim al-Zakzaky na kungiyar harkar m,usulinci ta IMN kuwa gwamnatin Najeriya ta ce maganar aikata babban laifi yana gaban kotu.

Gwamnati ta Najeriya ta danganta rahoton na hukumar kare 'yancin yin addini ta Amurka a matsayin wanda zai iya haddasa kiyayya tsakanin bangarorin addini na kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu