Sanarwar da ta fito daga gwmanatin tarayyar kasar ta ce duk wani dan kasar waje da ke zaune a cikin kasar ba bisa ka’ida ba, sannan kuma ya kasa yin rijista nan da ranar 12 ga watan janairu 2020, to za a kore su zuwa kasarsu.

Kakakin hukumar shiga da fice ta kasar Najeirya Sunday James ne ya bayyana hakan, sannan ya kara da cewa; Duk wani dan Najeriya wanda ya bayar da mafaka ga dan kasar wajen da yake zama ba bisa ka’ida ba, da sunan yana yi masa gadi, ko renon yara a gida da kuma aikatau, to zai iya fuskatar zaman kurkuku na shekaru bakwai, ko ya biyar tarar naira miliyan daya.

Har ila yau, Sunday James ya ce; Idan har aka kori yan wajen da su ka karya ka’idar da aka gndaya to ba za aske barinsu su shigo cikin kasar ba.