Majalisar dattawa a tarayyar Najriya ta bayyana goyon bayanta ga babban bankin kasar (CBN) bisa matakin da ya dauka na rage yawan kudaden da yake karba wajen mutane masu amfani da kayayyakin bankuna a kasar da kuma khidimomin da suke bayarwa ta kudade.

Shugaban kwamiti mai kula da bankuna a majalisar dattawan kasar Mr Victor Nwokolo ya bayyana cewa, babban bankin ya dauki matakin rage yawan kudaden da ake karba wajen masu hulda da bankuna a kasar ne saboda bukatar kwamitinsa na yin hakan.

A baya-bayan nan dai shugaban babban bankin na kasa, Mr Godwin Emefiele ya bayar da sanarwan cewa a halin yanzu amfani da na’urar ATM ba zai fi Naira 50 ba. Sai kuma musayar kudade ta hanyoyin sadarwar bankuna a kasar, idan kudaden basu kai naira 5,000 ba naira 10 ne.

Sannan daga 5001-50,000 ana chajin naira 25. Daga karshe musayar kudade daga naira dubu 50,000 zuwa sama kuma ana chajin naira 50.