Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Netanyahu Ya Ranta Cikin Na Kare Sakamakon Rokar Da Aka Harbo Daga Gaza


Firayi ministan haramtacciyar kasar Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ranta cikin na kare a lokacin da yake yakin neman zabe a kudancin Isra’ilan a jiya Laraba sakamakon harbo wani makami mai linzami da aka yi daga Zirin Gaza.

Gidan Talabijin din ‘Isra’ila’ ya ce an harbo makami mai linzami ne daga Gaza zuwa garin Ashkelon da ke kimanin kilomita 12 daga Zirin Gazan a daidai lokacin da Netanyahun yake yakin neman zabe, inda nan take gudu da shi daga wajen yakin neman zaben har sai bayan abubuwa sun lafa kafin ya dawo.

Wannan dais hi ne karo na biyu da hakan take faruwa da Netanyahu inda a watan Satumbar da ta gabata ma jami’an tsaronsa sun gudu da shi bayan an harbo wani makami mai linzami daga Gazan zuwa garin Ashdod inda yake yakin neman zaben.

Netanyahu din dai yana yakin neman zaben ci gaba da shugabancin jam’iyyar Likud mai tsaurin ra’ayi ne a zaben cikin gida da za a gudanar a yau sakamakon kiraye-kirayen da ake masa na ya sauka daga shugabancin jam’iyyar bayan rashin nasarar da jam’iyyar take ci gaba da fuskanta a zabubbukan da aka gudanar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu