Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Nigeria Ta Dakatar Da Kamfanin Jirgin Saman Turkiya Daga Sauka A Filayen Jirgin Saman Kasar Ta.


Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Nigeria ta sanar da dakatar da kamfanin jirgin sama na kasar Turkiya wato Turkish Air line daga gudanar da ayyukansa a fadin kasar saboda mummunar muamala da yake yiwa pasinjojin kasar.

Kamar yadda ya zo a wasikar da mukaddashin Directa Janar na hukumar NCAA ta Nigeria Abdullahi Sidi cewa gwamanti ta dauki wannan matakin ne saboda yawan korafe korafe da ake kai mata gamae da irin nuna halin ko in kula da pasinjojin suka kai mata na tsawon lokaci, inda jirgin ke zuwa da matafiya ba tare da kayansu ba.

Ya ci gaba da cewa lamarin ya kara muni ne a yan mwakannin nan inda kusan kashe 85 na matafiya da jirgin ke kawowa Nigeria suna sauka ne ba tare da kayansu ba, duk da tattaunawa da aka da mahukumtan kamfanin jirgin game da wannan matsala amma shiru kake ji kamar an shuka dusa.

Daga karshe ya nuna cewa wannan dakatarwa zai ci gaba har sai sanda kamfanin ya shirya sanyar jirgin sama babba wanda zai iya kwashe dukkan matafiya tare da kayansu a lokaci guda,yadda matafiya zai sauka tare da kayansa.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu