Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Nijar; An Fara Zaman Makokin Kisan Sojoji 71 Da ‘Yan Ta’adda Su Ka Yi


Gwamnatin kasar Nijar ta sanar da kwanaki uku na zaman makoki da alhinin sojojin kasar 71 da su ka kwanta dama, sanadiyyar wani mummunan harin ta’addanci.

Kungiyar ‘yan ta’adda ta masu riya cewa suna jihadi da ke yankin Sahel ce ta dauki nauyin kai hari a wani sansanin soja.
Kungiyar ‘yan ta’addar ta sanar da cewa; ta kai hari ne dai a kusa da garin Inates da ke kusa da iyaka da kasar Mali a ranar Alhamis. Bugu da kari kungiyar ta kuma ce sa’o’i masu yawa su ka dauka suna ruwan wuta akan sansanin sojan na Nijar, kuma sun yi awon gaba da makamai masu yawa.

Daga cikin kayan da su ka yi awon gaba da su, da akwai motoci 12, sannan kuma su ka cinnawa sansanin wuta lokacin da su ke ficewa.

Tun da fari gwamnatin Nijar ta tabbatar da cewa wasu mutanen 12 sun jikkata sanadiyyar wani hari da aka kai a yankin a farkon makon da ya shude.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu