Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Pakistan : An Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutumin Da Ya Baci Annabi (As)


A Pakistan, an yanke wa wani malamin jami'a da ya yi batanci ga Annabi Muhammad SAW hukuncin kisa.

Malamain jami'ar mai suna Junaid Hafeez, yana tsare ne a hannun hukuma bayan ya wallafa kalaman cin mutunci ga Manzon Allah a shafinsa na sada zumunta a 2013.
Lauyan da ke kare Junaid, ya ce za su daukaka kara kan hukuncin kotun.

Ita mai kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty Int, ta yi zargin rashin adalci a hukuncin, wanda ta bayyana a matsayin mai ban takaici.

Kasar Pakistan mai yawan al’umma miliyan 207 wadanda kasha 95% musulimi ne, ta tanadi dokar hukuncin kisa ga masu batanci ga addinin Islama.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu