Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Rasha Da Ukraine Sun Amince Janye Dakarunsu


Kasashen Rasha da kuma Ukraine sun amince sun janye dakarunsu daga yankuna guda uku da suke da takaddama a kai, kafin nan dad a karshen watan Maris na shekara 2020 mai shirin kamawa.

Wannan bayanin na kunshe ne a wata sanarwa da aka fitar yayin taron lalubo hanyoyin farfado da zaman lafaiya tsakanin bangarorin biyu wanda shuwagabannin kasashen ke halarta a birnin Paris.

A jiya Litini ne aka fara taron wanda Faransa da kuma Jamus ke shiga tsakani.
Taron dai zai kasance irinsa na farko tun bayan shekara 2016, inda kuma ake sa ran shugaba Vladimir Putin da Volodymyr Zelenskiy zasu gana a karon farko.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu