Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Rundunar Sa-Kai Ta Iraqi Ta Zargi Amurka Da Bai Wa ‘Yan Ta’adda Makamai


Rundunar sa-kai din ta Iraqi, ( Hashdus-sha’abi) ta fitar da wata sanarwa a jiya Litinin da a ciki ta bayyana cewa ta sami makaman Amurka a hannun ‘yan kungiyar ta’adda ta “Da’esh' a tsibirin “Hadhar” tare da jaddada cewa sojojin Amurkan ne su ke bai wa masu akidar kafirta musulmi makamai a kan tsaunukan Makhul.

Bayanin ya kuma kara da cewa; Sojojin na Amurka sun shata iyaka a yankin da ke kusa da sansaninsu a yammacin kasar, ta yadda ba su barin wani ya karace shi, don haka nan ne iyakar da ‘yan Da’esh su ke bacewa idan an biyo su.

Rundunar ta “Hashdu-Sha’abi” ta kuma ce; A nan gaba za su yi taho mu gama da sojojin Amurka a yankin da ya ke yammancin kasar.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu