Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sarkin Moroco Ya Ki Ganawa Da Saktaren Harakokin Wajen Amurka


Sarkin kasar Moroco Muhamad na shida ya ki amincewa da bukatar saktaren
harakokin wajen Amurka Mike Pampeo na ganawa da shi a Rabat babban birnin kasar
Tashar talabijin Rusiya Al-yaum ta habarta cewa a jiya alhamis ne saktaren harakokin wajen Amurka Mike Pampeo ya shiga birnin Rabat inda ya gana da Firai ministan kasar Sa'adu-ddin Usmany da babban daraktan dake kula da harakokin tsaron kasar Abdulatif Hamushi.

Rahoton ya ce saktaren harakokin wajen na Amurka ya bukaci ganawa da sarkin kasar ta Moroco Muhamad na shida amma har ya zuwa yanzu bai samu amsawa da fadar sarkin ba.sannan kuma babu wata liyafa da aka shiryawa saktaren harakokin wajen Amurka a daren jiya kamar yadda ake yi a baya.

Har ila yau duk da cewa a baya an shiga gudanar da taron manema labarai tsakanin ministan harakokin wajen kasar ta Maroco Naser Bourita da takwaransa na kasar Amurka Mike Pampeo, amma daga baya aka dage taron.

Wasu kafafen yada labarai sun habarta cewa saktaren harakokin wajen Amurka ya kai ziyara ne kasar ta Maroco da nufin mayar da alakar kasar da haramtacciyar kasar Isra'ila.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu