Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sayyid Nasrallah Ya Zargi Amurka Da Tsoma Baki A Zanga-zangar Da Ake Yi A Lebanon


Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi a jiya Juma’a, ya ce; A duk lokacin da al’ummar wata kasa suke gudanar da Zanga-zanga, za mu ga Amurka suna yi mata hawan kawara, domin amfani da ita su kai ga manufofinsu,akasin abin da wannan al’ummar ta ke so.

Sayyind Nasarllah ya yi ishara da Zanga-zangar da ake yi a cikin kasashen larabawa, da yankin Latin na Amurka da kuma Hong Kong da Amurkawan su ke tsoma baki a ciki.

Dangane da Zanga-zangar da ake yi a cikin Lebanon, Sayyid Nasarlalh ya ce; Mun irin yadda jami’an gwmanatin Amurka su ke Magana akai, daga cikinsu hadda sakataren harkokin waje Pempeo.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Amurka sun gina tunaninsu ne akan cewa; Zanga-zangar da ake yi a Lebanon ta kin jinin Iran da gwagwarmaya ce, alhali lamarin ba haka ya ke ba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu