Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban Kamfanin Boeing Ya Yi Murabus



Shugaban hamshaken kamfanin kera jiragen saman Amurka na Boieng, Dennis Muilenburg, ya yi murabus daga mukaminsa na shugabancin kamfanin dake ciki tsaka mai wuya.

tun bayan dakatar da jiragensa samfarin 737 Max, daga tashi da sauka a duk fadin duniya sakamakon hadarurutukan da sukayi a kasa da watanni biyar.

Kamfanin na Boeing din ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya Litini, inda tuni yam aye gurbin, shugaban kamfanin mai murabus da shugaban hukumar zartaswa ta kamfanin Dave Calhoun.

Hadarurukan da jiragen kamfanin samfarin 737 Max, wadanda suka haddasa mutuwar fasinjoji 346, sun jawo wa kamfanin mummunar koma bayan da bai taba fuskanta ba a cikin gomman shekaru.

Babu dai wani takamaiman lokacin da ake tsamanni za’a dawo da aiki da jiragen samfarin 737max a halin yanzu, lamarin da ya kawo wa kamfanonin jiragen sama da dama tsaiko a harkokinsu na jigilar fasinjoji.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu