Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban kasar Guine Bissau Ya Goyi Bayan Tsohon Fira Minista Sissoco Embla A Zabe Mai Zuwa


Shugaba Jose Mario Vaz ya nuna cikakken goyon bayansa ga tsohon fira ministan kasar Umaro Sissoco Embalo a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi a karshen wannan watan na Disamba.

Embalo wanda shi ma ya taba rike mukamin fira minista, ya lashe zabe ne bayan da ya yi takara da wani tsohon fira ministan Domingos Simoes Pereira.
A zaben da aka yi a ranar 24 ga watan Nuwamba, Sissoco Embalo ya zo na biyu da kaso 27.6% na jumillar kuri’un da aka kada, yayin da Pereira ya zo na farko da kaso 40.1%

Ya zuwa yanzu tsoffon shugabannin kasar ta Guine Bissau biyu ne su ke goyon Bayan Omaru Sissoco Embalo da su ne; Nuno Gomes Nabiam da Carlos Domingos Gomes.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu