Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban Kasar Iran Ya Kira Yi Da Ta Dauki Matakan Dakatar Da Amfani Da Kudin Amurka Na Dala


Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron da kasashen musulmi su ke yi a kasar Malysia ya ce; Duniyar musulmi tana fuskantar kalubale mai yawan gaske, don haka ya kamata ta dauki matakai da su ka hada da dakatar da amnfai da dalar Amurka.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma kara da cewa;lokaci ya yi da al’ummar musulmi za su yi aiki tare domin ganin sun zama wani karfi a duniya, don haka ya zama wajibi su fito da wani tsari domin cimma wannan manufa.

Dr. Hassan Rauhani ya kuma yi ishara da yadda Amurkan take amfani da kakaba takunkumi a matsayin wani makami na siyasa, ta hanyar amfani da kudinta na dala da ake amfani da shi a cikin cibiyoyin kudi da duniya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu