Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugaban Kasar Syria Asad Ya Zargi Amurka Da Turkiya Da Satar Man fetur Din Kasarsa


A wata hira da ya yi da gidan talbijin din kasar China shugaban kasar Syria Bashar Asad ya sanar cewa shirin sake gina kasar ya fara aiki sai dai akwai bukatar masu sanya hannayen jari sosai daga ciki da wajen kasar. Ya kara da cewa yaki da ‘yan ta’adda shimfida ne na kalubalantar Amurka , domin kasashen Turkiya da Amurka suna ci gaba da satar arzikin man fetur da Allaha ya huwace mata.

Har ila yau ya nuna fatansa na ganin masu sanya hannayen jari na kasar China sun duba yiyuwar sanya hannayen jarinsu a kasuwar kasar. Yanzu haka gwamnati ta fara tattaunawa da wasu kamfanomnin kasar China domin sake gina yankunan da aka yantar daga mamayar yan ta’adda.

Da yake bayani game da kasancewar Amurka a kasar ba bisa doka ba Asad ya nuna cewa kasancewar Amurka a Syria ba ya kan doka, kuma babban abin da ya fi muhimmacin wajen kalubalantar kasancewar dakarun waje a kasar shi ne tunbuke toshen ta’adanci , domin akwai kungiyoyi da ke karkashin kulawar Amurka dake gudanar da ayyukansu a kasar.

Daga karshe ya yi Ishara game da hadin gwiwa tsakanin Amurka da Turkiya a Arewacin kasar , inda yanzu haka Amurka na ci gaba da sace man fetur din kasar tana sayarwa kasar Turkiya wadda ita ma tana da hannun wajen sa ta da siyar da man kasar da hadin guiwa kungiyoyin yan ta’adda.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu