Dr. Ali Larijani wanda ya fitar da sakon taya murnar zagayowar kirsimeti ga ‘yan majalisar mabiya addinin kirista a yau Talata, ya yi fatan yin bukukuwan kirsimetin da kuma sabuwar shekara ga mabiya addinin kirista cikin zaman lafiya.

Dr. Ali Larijani ya kara da cewa; Na yi imani da cewa; Adalci da zaman lafiya irin wadanda annabi Allah, annabi Isa (a.s) ya yi wa’azi akansu, za su tabbata, domin abubuwa ne masu yiyuwa.”

Shugaban majalisar shawarar musuluncin ta Iran ya kara da cewa; Ta hanyar tattaunawa da cudanyar juna ne mabiya saukakkun addinai za su iya cimma zaman lafiya.