Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya kai wata ziyarar ba zata zuwa kasar Tunusiya don tattauna batun yiyuwar tsagaita wuta a kasar Libiya inda gwamnatin Turkiyya take taimakawa gwamnatin kasar da take samun goyon kasashen duniya.

A wata ganawa da maneman labarai da yayi da takwararsa na kasar Tunusiyan Kais Saied, Erdogan ya ce sun tattauna hanyoyi da za a bi wajen ganin an tsagaita wuta a Libiyan da kuma dawowa ga tattaunawa ta siyasa, sai dai kuma ya sanar da aniyar gwamnatinsa ta aikawa da sojoji zuwa Libiyan matukar dai gwamnatin ta bukaci hakan.

Ziyarar ta Erdogan ta zo ne wata guda bayan Turkiyya da Libiya sun sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi kan harkar tsaro da taimako na soji buga da karin kan lamurran da suka shafi kan iyakoki na ruwa.

Turkiyya din dai tana goyon bayan gwamnatin Fayez al-Serraj da duniya ta amince da ita lamarin da ya sanya ‘yan tawayen kasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar suke nuna yatsar zargi ga Turkiyya a matsayin wacce take rura wutar yaki a Libiya da kuma alkawarin kai wa jiragenta hari wadanda tace suna dakon makamai zuwa Libiyan.