Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugabanin G5 Sahel Za Su Yi Taron Gaggawa A Nijar


A gobe Lahadi ne ake san ran shugabanin kasashen yankin sahel wato G5 Sahel za su gudanar da taron gaggawa a birin Yamai domin tattaunawa kan bukatar Shugaba Macron na Faransa na neman a fayyace masa akwai bukatar zaman dakarun kasarsa a yankin na Sahel.

A baya dai an shirya gudanar da wannan taro ne a birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso, to amma bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa sojojin na Nijer wanda ya yi sanadiyar mutuwar sama da 70 daga cikinsu , aka maida taron birnin Yamai domin nuna goyon baya da kuma jajantawa al’ummar kasar ta Nijer.

A ranar 10 ga watan Dicembar da ta gabata ce wasu mahara dauke da mugan makamai suka kai hari kan barikin sojan kasar na Inates dake kai iyaka da kasar Mali, lamarin da ya yi salwantar rayukan sojojin Nijer sama da 70 da kuma jikkatar wasu 12 na daban.

Tuni dai kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai harin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu