Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugabannin Addini A Habasha Sun Bukaci A Hada Kai Bayan Harin Da Aka Kai A Masallaci.


Cibiyar samar da fahimta tsakanin Addinai a kasar Ethiopia ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta hada kai da alumomi domin kare wuraren ibada a kasar, bayan da wasu suka kai hari kan wani masallaci da ke lardin Amhara. Kana sun bukaci jama’a da su taimaka wajen sake gina masallacin da wuraren kasuwanci da aka kona a Garin Motta. Batun rikicin kabilanci na barazana ga sabon tsarin a Fira ministan kasar Abiy Ahmed ke kokarin bullowa da shi.

Kakakin yankin na Amhara Genet Yirsaw ya bayyana cewa tuni aka cafke mutane 5 da ake zarginsu da hannu wajen kona masallacin. Ya kara da cewa akwai wata coci da ke da nisan kilo mita 377 da birnin Adis Ababa da aka yi yunkurin kona ta, sai dai ya zuwa yanzu babu karin bayani game da wanda ke da alhakin shirya kai harin.

A nasa bangaren shugaban cibiyar musulunci da ke yankin na Amhara ya bayyana cewa Harin na Motta na ba za ta ne, kuma an kona shagunan kasuwanci na Musulmi da kuma lalalata wasu gine gine.

Daga karshe shugabannin addini sun yi kira ga matasa da su guji daukar ramuwar gayya da zai iya jawo rikicin addini. Yanzu haka dai shugaban kasar Ahmen Abiy ya yi tir da kai harin kuma ya ce ba za su bar tsagera su canza tarin kasar na hakuri da juna tsakanin mabiya addinai a kasar ba.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu