Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Shugabannin Afirka Sun Jaddada Muhimmancin Yakar Ta'addanci


Shugabannin kasashen Afirka da wasu wakilan sassan kasa da kasa, sun jaddada muhimmancin zage damtse ga aikin yaki da ta'addanci, da tabbatar da tsaro, a matsayin hanyar wanzar da ci gaban nahiyar.
An dai gabatar da wannan shawara ne a jiya Laraba, yayin kaddamar da taron, birnin Aswan na kasar Masar kan tattauna dabarun wanzar da zaman lafiya da ci gaban nahiyar Afirka.

Taron na Aswan dai zai maida hankali ga batutuwa da suka kunshi sake gina yankuna bayan tashe-tashen hankula, da raya ilimi, da sauyin yanayi, da kuma ci gaba mai dorewa a Afirka.

Da yake gabatar da jawabin bude taron, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi, ya yi kira ga daukacin masu ruwa da tsaki, da su kara azama wajen aiwatar da matakan yaki da ta'addanci a dukkanin sassan duniya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu