Ma’aikatar tsaro a jamhuriyar Nijar, ta sanar da cewa sojojin kasar 71 ne suka kwanta-dama, kana wasu 12 suka raunana yayin da wasu da dama suka bata, a wani harin ta’addanci da aka kai masu a yankin Inates a jihar Tillabery dake kudancin kasar a kusa da iyaka da kasar Mali da yammacin ranar Talata.

Wata sanarwa da aka karanto a gidan talabijin din kasar, ta ce gungun maharan da aka kiyasta sun kai daruruwa, sun kai harin da muggan makamai, da hare haren kunar bakin wake da motoci da kuma Babura.

Sanarwar ta kuma isar da ta’aziya ga iyalan sojojin da suka kwanta dama da kuma fatan sauki ga wadanda suka raunana.
Wannan dai shi ne harin ta’addanci mafi muni da sojojin kasar suka taba fuskanta tun bayan da mayakan dake ikirari da sunan jihadi suka fara kai kasar hare hare a cikin shekara 2015.

Shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu, ya dawo gida a cikin daren jiya bayan ya katse ziyarar da ya ke a birnin Alkahira na kasar Masar, inda ya ke halartar wani taro kan tsaro da ci gaban Afrika.

Babu dai wata kungiya data dauki alhakin kai harin, saidai yankin ya yi kaurin suna wajen fusnkatar hare haren kungiyar nan dake kiran kanta reshen kungiyar ‘yan ta’adda ta (IS) a yankin Sahara.