Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sudan; Hambararren Shugaban Kasar Sudan Ya Fuskanci Tuhuma Akan Juyin Mulkin 1989


A ranar Talata dayya gabata ne hambararren shugaban kasar na Sudan Umar Hassan al-Bashir ya fuskanci tambayoyi da tuhuma akan rawar da ya taka a lokacin juyin mulkin 1989 wanda ya dora shi kan mulki.

Boren da al’ummar kasar ta Sudan su ka yi ne ya kai ga kifar da gwamnatinsa a cikin watan Aprilu, kuma ya fara fuskantar shari’a a cikin watan Mayu bisa laifin da ya ke da alaka da kashe masu Zanga-zanga.
Wasu daga cikin tuhume-tuhumen da ake yi wa hambararren shugaban kasar ta Sudan, sun hada da karbar kudade daga wasu kasashen waje.

Wani daga cikin lauyoyin da su ke bayar da kariya ga tsohon shugaban kasar ta Sudan, Hassan al-Amin ya bayyana cewa; tuhumar da ake yi wa wanda yake bai wa kariya akan juyin mulkin, ta siyasa ce domin shekaru 30 sun shude daga afkuwarsa.
Lauyan ya ci gaba da cewa; Mun bukaci al-Bashir da ya kauracewa zama da masu yi masa tambayoyi.

Ita kuwa kotun manyan laifuka ta duniya tana son a mika ma ta hambararren shugaban kasar ta Sudan, bisa takardar kamun da ta fitar a 2009 zuwa 2010. Ana tuhumar al-Bashir da laifin yin kisan kiyashi a yanin Darfur.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu