Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sudan : Kotu Ta Daure Tsohon Shugaba Al-Bashir


Wata Kotu a birnin khartum ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu ga tsohon Shugaban kasar Omar El Bashir bayan tabbatar da tuhumar da ake yi masa na karbar rashawa tareda mallakar kudadden ketare ba bisa ka’ida ba.

Tashar Talabijin din Sky News ta ruwaito cewa da safiyar yau asabar ne wata kotu dake birnin Khartum ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu ga hambararen shugaban kasar Omar El-Bashir wanda kuma aka fice da shi zuwa gidan yarin gyara halinka na dattijai kamar yadda dokar kasar ta tanada, idan mutum ya fice shekaru 70 a Duniya to a kan kai shi wannan gidan kaso na gyara halinka.

Tsohon Shugaban kasar Omar El Beshir da ya mulki kasar Sudan tsawon shekaru 30, ya na daga cikin shugabani da suka jima a kan karagar mulki a Afrika.

Lauyoyi dake kare tsohon Shugaban sun bayyana cewa ba su fatan kotu ta yiwa El Bashir sassauci,kasancewar sa soji,banda haka da alama za su daukaka kara nan gaba dangane da wannan hukunci.

Gwamnatin rikon kwarya da ta hada sojoji da farraren hula a karkashin shugabancin firaminista farar hula na kokarin dimke barraka da aka samu a kasar ta Sudan, tun bayan faduwar gwamnatin tsohon Shugaban kasar Omar El Bashir.

A halin da ake ciki dai, kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa na son gwamnatin ta Sudan ta mika mata hambararen shugaban kasar domin ya fuskanci tuhume-tuhumen da ake yi masa na yiwa al'ummar yankin Darfur kisan kiyashi.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu