Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sudan ta Kudu : Za'a Kafa Gwamnatin Hadaka A Watan Fabrairu


Shugaban Salva Kiir na Sudan ta Kudu, da madugun ‘yan adawa na kasar Riek Mashar, sun amince da kafa gwamnati hadin kan kasa kafin karshen watan Fabrairu na shekara mai zuwa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da shugabannin kasashen yankin suka dibar masu wa’adin na kwanaki 100 na su kafa gwamnatin.

Bangarorin sun amince da hakan ne yayin wata ganawa da sukayi ta kud da kud.
Yayin ganawar shugaba Kiir, ya bayyana cewa kafa gwamnatin bayan kwanakin 100, duk da cewa bangarorin bayu basu fahimci junansu ba game da batun adadin jihohin kasar ba, wanda daya ne daga cikin batutuwan da suke da babban sabani a kai.

A wani labarin kuma Amurka ta sanar a jiya Litini, da kakaba takunkumi ga wasu ministocin Sudan ta kudun guda biyu da ta ce suna kawo cikas ga yunkurin samar da zaman lafiya a kasar dake fama da yaki tun cikin shekara 2013.

Ministocin guda biyu da AMurka ta kakaba wa takunkumi sun hada da ministan tsaro na kasar da kuma na harkokin gwamanti.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu