Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Sudan Ta Mika Mayakan Boko Haram 6 Ga Gwamnatin Chadi


Hukumomin tsaron kasar Sudan sun sanar da damka mayakan kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram su 6 ga gwamnatin kasar Chadi karkashin tsarin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Kakakin ma'aikatar tsaron Sudan Amer Mohamed Al-Hassan, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, jami'an sojoji masu binciken sirri sun mika mayakan Boko Haram 6 wadanda suke dauke da takardun fasfo na kasar Chadi a cikin yankunan kasar Sudan.

Ya kara da cewa, daga bisani an mika mutanen da aka cafke ga hukumomin tsaron N'djamena karkashin tsarin yarjejeniyar hadin gwiwar tsaron kan iyakoki wanda kasashen Sudan, Libya, Nijer da Chadi suka rattabawa hannu.

Tun daga shekarar 2008, kungiyar Boko Haram ta fara kaddamar da ayyukanta a kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu