Firaministan kasar Sudan ya ce cikin kankanan lokaci Sojojin kasarsa za su dawo gida daga kasar Yemen

Tashar Talabijin din Aljazera ta ruwaito firaministan kasar Sudan Abdallah Hamdouk na cewa akwai sojojin kasar Sudan dubu 25 a kasar Yemen, kuma manufar gwamnatin hadin kan kasar sudan shi ne dawo da wadannan sojoji cikin iyalensu a kankanan lokaci.

Hamduk ya kara da cewa tattaunawa ita ce hanya daya cilo na warware rikicin yemen da kawo karshen yaki a kasar.

Jam'iyun siyasa da kungiyoyin fararen hula a sudan din sun bukaci gwamnatin rikon kwaryar kasar da ta gaggauta janye dakarun kasar daga cikin kawancen saudiyar dake yakin wuce gona da iri a kasar Yemen.

Kafin hakan dai gwamnatin hadin kan kasar ta bayyana shirinta na janye dakarun kasar daga yemen.

Tun a shekarar 2015 ne gwamnatin kasar Sudan ta tura dakarunta zuwa kasar yemen da nufin hadewa da kawancen saudiya na kaddamar da yakin wuce gona da iri kan al'ummar kasar, saidai wannan lamarin ya fuskanci adawa daga al'ummar kasar ta Sudan.