Kasar ta Rwanda ta rattaba hannu ne akan yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Paris St Germain ta kasar Farnasa, domin tallata wuraren yawon bude ido da ake da su da kuma kayan da ake kerawa a kasar.
Shugabar hukumar raya kasar Rwanda Clare Akamanzi wacce ta sanar da yarjejeniyar, ta kara da cewa; sun yi hakan ne saboda kyakkyawar mahanagar da kungiyar kwallon kafar take da ita akan kasar ta Rwanda.

Tare da cewa gwamnatin kasar ta Rwanda ba ta bayyana kudin da za ta biya Kulub din ba, sai dai wata majiya daga can birnin Paris ta ce, kudaden suna a tsakanin Euro miliyan 8 zuwa 10 ne.

A shafinsa na Twitter, Kulub din na PSG ya ce; Muna kiran duniya baki daya da ta shiga a dama da ita wajen samar da gagarumin sauyi a kasar Rawanda.”
Wasu bangarori na tallata kasar ta Rwanda zai kunshi sanya hotuna da kayyaykin da ake kerawa a kasar Rwanda a cikin allunan talla da ke filin wasan kungiyar kwallon kafar, da kuma jikin jakunkuna da sauran kayayyakin da bangaren mata na kulub ne suke amfani da su.

A shekarar da ta gabata dai kasar ta Rwanda ta kulla irin wannan yarjejeniyar ne da Kulub din Arsenal na kasar Birtaniya.
A shekarar 2018 kadai kasar Rwanda ta samu kudaden shiga ta hanyar yawon bude ido da su ka kai dalar Amurka miliyan 380. A bana ana hasashen za ta sami dalar Amurka miliyan 405.