Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

*TARIHIN SAYYID IBRAHEEM YAQOUB AL-ZAK-ZAKY (H) DA HARKAR MUSULUNCI TANA NIGERIA 🇳🇬*


 
TARIHIN SAYYID IBRAHEEM YAQOUB AL-ZAK-ZAKY (H) DA HARKAR MUSULUNCI TANA NIGERIA 🇳🇬

Daga:- Muhmmad Suleiman Kd

Bisimillahir Rahamanir Raheem

Amma kafin inshiga cikin bayani dangane da tarihin Sayyeed Zakzaky (H) akwai shimfida ko gabatarwa a taqaice. Da farko dai rubutu ko bayani dangane da Sayeed Zakzaky (H) wani fage ne mai fadin gaske, Wanda mutum ba zai iya kewayawa da shi ba. Domin Sayyeed Zakzaky (H) wata baiwa ce da kuma kyauta ta musamman da Allah (T) ya bai wa wannan nahiya da muke ciki. Da a ce mutum zai yi tunani kuma ya duba da kyau, zai ga cewa a duka baiwowin da Allah (T) ya yi wa wannan nahiya da muke ciki, a wannan zamanin, to suna komawa bayan wannan baiwa ta Sayyid Zakzaky (H) ne. Ta yiyu wani ya ja da hakan amma iyakar maganar ke nan.

Misali kamar a ce lokacin Shehu Usman Dan Fodiyo ne, akwai baiwar da Allah (T) ya yi wa al'ummar lokacin, wadda ta kai kyauta da ya bayar ta Shahe Usman Dan Fodiyo? Mutum ya tambayi tarihin wannan nahiya, ya ba shi ansa. Cewa tun bayan zuwan 'yan mulkin-mallaka a wannan nahiya tamu, da abubuwan da suka yi na nade shimfidar da Shehu Usman ya shimfida, an samu wani malami da ya yi da'awa, kuma ya dake a kan da'awar tsawon shekaru, a kan cewa a koma kan nizamin da Shehu Usman ya shimfida, a kan haka ya fuskanci jarabawowi daban-daban, shi da wadanda suka amsa masa da'awar?

Kai da ma wannan qasar da muke ciki ba, qasashen Nan maqwabta da suke qarqashin daular Usmaniyya gabanin 'yan mulkin-mallaka su yayyanka qasashen. To mutum ya duba da aka yayyanka din, akwai wani malami a cikin wadannan qasashen wanda yake da'awa ta gwagawrmayar tabbatar da addini shigen ta Shehu Usman Dan Fodiyo, kamar yadda Sayyeed Zakzaky (H) yake yi a nan?

Haka nan mu dauki fahimta ta Ahlul Bait (AS), wato tamassuki da wilayar Ahlul Bait (AS) wacce kasa ce daga cikin qasashen ahlus Sunnah da mutum ya sani a yau, wadda a cikinta aka samu want malami, wanda al-barkacinsa, Kuma sakamakonsa aka samu fahimta, kuma cikin 'yan shekaru kadan adadi mai yawan gaske na mutane maza da mata, yara da manya suka yi istibsari (wato fahimtar Ahlul Bait (AS) da kuma riqo da su) kamar wannan qasar da muke ciki. Lallai in akwai zan so in San qasar. To ire-iren wadannan misalsalai suna da yawa, wadanda ke nuna lallai Sayyeed Zakzaky (H) baiwa CE ta musamman da Allah (T) ya yi wa wannan nahiya da muke ciki.

Kuma in da mutum zai yi tunani kuma ya duba wannan al'amari na Sayeed Zakzaky (H) tun daga lokacin da ya soma da'awa zuwa yanzu da irin matsalolin da jarabawowi da ya fuskanta masu yawa, musamman ma ta fuskacin masu tafi da iko na gwamnatoci daban-daban da nufin murqushe da'awar da kuma kashe shi, in dai mutum bai ce Allah ba, to ba abin da zai ce. Wannan yin Allah (T) ne. Domin shi tabbatar da addini, wani abu ne wanda yake hannun Allah (T) amma ya saba yana amfani da mutane ne  wajen tabbatar da addini ko jaddada shi. Kuma za6in in da addinin zai tabbata zai yi amfani da shi domin tabbatar da addinin, da za6in in da addinin zai tabbata, da kuma za6in lokacin da zai tabbatar da addini, duk a hannu Allah (T) suke.

Soboda haka in Allah (T) ya za6i wanda zai yi amfani da shi domin tabbatar da addini ko jaddada shi. An so ko ba a so ba, an yarda ko da a yarda ba, da shi din zai yi amfani, Kuma duk wani qulle-qulle ko makirce-makirce, ko zagon qasa, ba su isa su hana abin da Allah (T) ya yi nufi ba. Kuma irin wadannan bayi da Allah (T) kan za6a yana ba su kariya ta musamman daga wajensa. Mu duba yanqurin kisan da Sayyeed Zakzaky (H) ya fuskanta a lokuta daban-daban tun lokacin yana dalibi a jami'ar har ya zuwa yau. Saboda haka al'amarin Sayyeed (H) al-amarin ne na Allah (T).

Ko da ba abubuwa na badinance, akwai abubuwa na zahirance da suke nuna cewa lallai Sayyeed Zakzaky (H) da kuma da'awar da yake yi al'amarin ne na Allah (T). Ga wasu daga ciki.

(1) Ayoyi daban-daban, ta kuma fuskoki daban-daban, a lokuta daban-daban da suka faru a cikin da'awar. Misali wasu ayoyi da aka gani a wasu lokuta ga Shuhada'u na wanna gwagawrmaya.

(2) Ishara daga wasu malamai da kuma bayin Allah (T) dangane da Sayyeed Zakzaky (H) da kuma da'awarsa.

(3) Alamomi na kan hanya, wato na abubuwa da suka same shi kuma mabiyansa, wato alamomi wanda suka nuna lallai mutum na kan hanyar Annabawa da kuma masu tajdidan addini.

(4) Mafarkai na ma'asumin (AS), wanda 'yan uwa da dama wadanda ba 'yan uwa ba suka yi a lokuta daban-daban dangane da Sayyeed da kuma da'awarsa. Misali ka ga wani ya yi mafarkin da manzon Allah (S) ko daya daga cikin A'imma (AS) ya ce masa tafarkin da Sayyeed yake kai, tafarki ne na dai-dai, saboda haka ya bi shi, ya kuwa kasance tare da shi, ko kuma Ma'asu (AS) ya nuna masa cewa lallai abin da Sayyeed yake a kai, shi ne shiriya da dai makamantarsu. Ta yiwu wani ya ce ai mafarki ba hujja ba ne, na'am amma ai bushara ne ko?

(5) Yanqurin kau da shi da kuma da'awar, amma haka ya gafara, da kuma qarshen wadanda suka cutar da shi da kuma mabiyansa. Mutum ya waiwaya baya ya gani, ya ga qarshen wadanda suka cutar da shi, ta fuskacin masu tafi da iko da mutanen gari da dai sauransu ya ga ya Allah (T) ya yi da su tun a nan daniya. Wanda wannan dai baki daya na wadannan abubuwa da aka kawo na badinance da kuma zahirance yana nuna cewa lallai al'amarin Sayyeed (H), in dai mutum bai ne wannan yin Allah ba ne, to ba abin da mutum zai ce. Wannan ke nan bai a taqaice dangane da wannan shimfida da kuma gabatarwa.

Kubiyo mu a rubutu na gaba domin cigaba da wannan rubutu na tarihin Sayyeed Zakzaky (H) da harkar musulunci

FreeSayeed Zakzaky Dolee

Daga Muhmmad Suleiman Kd

Kaduna press

KNPRSCD 1⃣3⃣

Post a Comment

0 Comments

Close Menu