Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

Tawagar Likitocin Japan Za Ta Fara Gwajin Wata Allurar Riga Kafin Ebola A Congo


Wata tawagar kwararun likitocin kasar Japon, ta isa a kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Congo, da nufin gwada wata allurar riga kafin cutar ebola.
Masu bincike na sashen kimiyar kiwan lafiya na jami’ar Tokyo ne suka samar da allurar.

A cen dai an gwada allurar ga birai, saidai har kawo yanzu ba’a gwada ta ba ga dan adam.

Wani kwarare kan cututuka masu saurin yaduwa na kasar Japon, wanda ya taimaka wajen hada maganin ya bayana cewa akwai kyakyawan fata na a samu wani sabon maganin riga kafin cutar ta ebola.
Za’a dai fara gwajin maganin ga mutane 30 masu cikakar lafiya wadanda suka bada kansu don yin gwajin.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu