Filing Talla

Filing Talla Ga Mai Bukata Sai Ya Tuntube Mu

TUNAWA DA WAQI'O'IN 12/12 ZUWA NA FREE ZAKZAKIY A DA'IRAR KADUNA

YAN UWA SUN KOYAWA DUNIYA YADDA AKE KARE JAGORA...
-KADUNA PRESS.

Tunawa da waqi'o'in Harka Islamiyya a Da'irar Kaduna,
A yau lahadi 22/12/2019 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzakiy (H) na Da'irar Kaduna da kewaye suka shirya kuma suka gudanar da bikin tunawa da waqi'o'in da suka faru a harkar musulumci kama daga ta sha biyu ga watan sha biyu wato 12-14/12/2015 zuwa ta ranar talata da ranar ashura ta shekarar 2016 da wasu ba'adin waqi'o'in muzaharorin Free Zakzakiy da suka afku.

Taron wanda aka gudanar a hayin banki kawo Kaduna ya samu halartar 'yan uwa daga sassa daban-daban na Da'irar Kaduna.
A yayin gabatar da wannan taron anbukaci wasu ba'adin 'yan uwan da wadannan waqi'o'in suka afku akan idonsu domin 'yan uwa da sauran al'umma su darastu da darussan dake cikin waqi'o'in.
A tun bayan bude taron da addu'a babu bata lokaci aka Fara gabatar da 'yan uwan daya bayan daya,
'yar uwa Bilkisu m. Sahabi ce ta Fara abato abubuwan da suka faru akan idonta a waqi'ar Zaria wacce akayi a gyallesu inda Sheikh Zakzakiy yake da zama a wancan lokacin, Bilkisu tayi bayanin yadda jami'an tsaron Nigeria suka dinga cin mutumcin 'yan uwa musamman sistoci ba-a-da bayan sun kashe wadanda suka iya kashewa, malama Bilkisu tayi bayani mai tsawon gaske.
A cikin wadanda sukayi bayani a muhallin akwai wanda yayi bayani a bisa waqi'ar Hussainiyya bakiyyatullah tayadda cikin bayaninsa ya yace lallai jami'an tsaron da suka kawo wannan harin na Hussainiyya ba na kasarnan ne kawai ba domin a yayin da ake basu umarni a muhallin ba koda yaushe ake musu turanci ba, domin inda ace turanci ne zamuji abinda ake fada musu, tun lokacin da suka shiga gidan man dake daura da Hussainiyya mukaji ana basu umarni da wani yare na daban.

An gayyaci 'yan uwa daban-daban daga sassan jihar ta Kaduna domin gabatar da jawabai a bisa abubuwan da suka faru din.

A karshe aka gayyaci wakilin 'yan uwa na Da'irar Kaduna Sheikh Aliyu Tirmidhiy domin gabatar jawabi da ta'aliqi akan bayanan da 'yan uwan suka gabatar.
A cikin jawabinsa Mal. Tirmidhiy yace lallai 'yan uwa sun nunawa duniya da al'ummar cikinta yanda ake bayar da kariya ake bayar da rayuwa domin kare Jagora, ta yadda 'yan uwan Basu iya barin gyallesu ba sai bayan da aka ce musu Sayyid ya fita daga gyallesu, ba tare da makami ba suka iya jurewa suka jajirce suka hana jami'an tsaron isowa ga Sayyid har na tsawon kwana uku,
Sheikh Zakzakiy ba kawai makami bane a'a Shi Jagora be, domin Malamai ana iya samun dubbunansu amman Jagora guda daya akeyi saboda haka Shi Sayyid Jagora be, inji Mal. Tirmidhiy.

Kamar yadda duniya ta sani kuma take gani shine cewa bamu lamunta ba kuma bamu amince ba da irin abubuwan da wannan hukumomi keyi mana na daga muzgunawa da cin mutumci, kuma tabbace hakika zamu cigaba da fitowa, babu kakkautawa, sannan zamu cigaba da daukar matakan hankali irin wadanda suka dace da shari'a domin ganin cewa Jagoran mu yayi Free.
A karshe akayi addu'a aka sallami kowa.
-KNPRSCD 06.
-Jabeer Bin Said Al'ansariy.
-Kaduna Press.

Post a Comment

0 Comments

Close Menu